Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA -Ko a jiya ma dubun dubatan mutane ne suka yi zanga zangar a birnin Khartum domin kin amincewa da juyin mulki da sojoji suka yi, inda sojoji suka yi amfani da harsashi mai raid a haki mai sa hawaye wajen tarwatsasu , lamarin da yayi sanadiyar jikkata adadi mai yawa,
Masu zanga-zangar sun sha Alwashin ci gaba da hawa kan tituna har sai sun ga bayan mulkin soji a kasar, dubban mutane dake fitowa zanga zangar na daga cikin abin da ke kara daukar hankali da kuma kara mata armashi a idon duniya.
342/